26 Agusta 2024 - 09:17
Cikakken Jawabin Sayyid Hasan Nasrallah Dangane Harin Maida Martani Da Kungiyar Hisbulla Ta Fara Yau Akan Is’raila Bisa Kashe Kwamandanta Da Ta Yi.

Sakatare Janar na kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon, yayi bayani sa'o'i kadan bayan fara gagarumin martani na farko na kungiyar dangane da ramuwa ga ayyukan ta'addancin da gwamnatin sahyoniyawan sahyoniya ta yi a baya-bayan nan a shahadantar da Fu’ad Shukri, daya daga cikin kwamandojin gwagwarmaya a yankunan kudancin birnin Beirut.

Sayyid Hassan Nasrallah: Mun sanya wa Aikinmu na yau sunan (Arbaeen)

Sakatare Janar na kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon, yayi bayani sa'o'i kadan bayan fara gagarumin martani na farko na kungiyar dangane da ramuwa ga ayyukan ta'addancin da gwamnatin sahyoniyawan sahyoniya ta yi a baya-bayan nan a shahadantar da Fu’ad Shukri, daya daga cikin kwamandojin gwagwarmaya a yankunan kudancin birnin Beirut.

A farkon jawabin Sayyid Hasan Nasrallah ya ce: A yau ya zama wajibi mu yi ta'aziyya ga al'ummar Lebanon abar kauna, da gwamnatin kasar Lebanon da dukkanin kungiyoyin gwagwarmaya kan rasuwar Salim Al-Hus. Ya kasance babban alama ta kasa, ya kasance mai tsabta da gaskiya, ya kasance mai gwagwarmaya. Duk mun san cewa shugaba Al-Hus shi ne shugaban kasar Labanon a shekara ta 2000 kuma ya goyi bayan gwagwarmaya. Muna mika ta'aziyyarmu ga daukacin al'umma da 'yan uwa bisa rasuwar wannan babban jigo na kasa kuma mai kishin kasa.

Ina mika gaisuwa ga al'ummar kasar Labanon, musamman mutanen kudu da Dhahiyah. Wadanda suka dauki babban nauyi a watanni 11 da suka gabata a fagen goyon bayan Falasdinu.

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon yaci gaba da cewa: Muna rokon Allah ya sakawa al'ummar kudancin kasar bias hakuri da kokarin da suke yi da gwagwarmaya. Ina kuma mika gaisuwa ga ’yan uwa mujahidai da masu gwagwarmaya tare da gode musu bisa gaskiya da sadaukarwa. Ina mika gaisuwa ga dukkanin dakarun gwagwarmaya a Gaza, Yemen, Yammacin Kogin Jordan da Iraki da kuma ko'ina cikin duniya masu goyon bayan wannan gwagwarmaya mai daraja.

Don kiyaye ma'aunin ci baya, dole ne mu mayar da martani kuma ba za mu iya barin abokan gaba su ketare jajayen layukan ba. Kamar yadda kuka sani, kuma kowa ya sani, makiya Isra'ilawa sun kaddamar da hari a yankin kudancin kasar makonnin da suka gabata, sun ketara iyaka a yankunan kudancin kasar suka jefa bama-bamai a wani shahararren gini, wanda ya kai ga shahadar fararen hula da dama tare da kashe babban Mujahid Haj Fu’ad Shukri.

Abun da aka saba ne cewa gwagwarmaya don daidaita ramuwa zata mayar da martani ga wannan zalunci, kuma wannan lamari ne wanda ba a iya kauda kai akansa ba. A yau na fito fili ina mai tabbatar da cewa Ina amsa wannan tambayar me yasa aka jinkirta martanin. Mun sanyawa harinmu nay au sunan.

Tabbas, akwai dalilai na jinkirin yin martani. Bayan shahadar Fu’ad Shukri dukkan mun shirya. Na farko, yawan shirye-shiryen soji, fasaha, kasa, iska da teku na Amurka da Isra'ila ya kai kololuwar sosai don haka gaggawar aiwatar da martanin zai iya kaiwa ga rashin cin nasara.

Na biyu, jinkirin kansa, watau tsawaita shi, yana daga cikin sashen ukuba ga makiya. Wannan shiri da gajiyawar tattalin arziki da soji ya kasance ci gabansa mai amfani ne don yanzu suna jiran martanin Iran da Yemen.

Na uku, akwai bukatar tattaunawa da bincike tare da sauran bangarori, cewa dukkansu zasu mayar da martani a tare ne ko a ware.

Na hudu, lokacin da muka kusanci mayar da martanin.. Daya daga cikin dalilan da suka sa Amurka mai aikata laifuka ke kawo batun tattaunawa a yayin da ake fuskantar babban rikici ne.. Muna jiran sakamakon wannan tattaunawar kuma mun ba da isasshen lokaci.

An samar da wannan dama kuma ta bayyana cewa Netanyahu yana da sabbin sharudda kuma Amurka ma ta amince da shi, kuma ko ta yaya sun yi amfani da lokacinsu.

A sakamakon duk waɗannan abubuwan, mun yanke shawarar mayar da martani ga ayyukanmu a ware kuma mun bari kowane bangare ya yanke shawarar lokacin da kuma yadda zai mayarda martani.

A daya bangaren kuma, wadannan tattaunawar suna da sarkakiya, kuma idan Amurka na son dakatar da yakin, to za ta iya dora laifin harin ga Netanyahu.

A gefe guda, mun amince da yin aiki a cikin tsarin shirye-shiryen. A matsayinmu na gwagwarmaya, ba mu kasance a shirye don a jinkirta mayar da martani ba, kuma yanayin da ke cikin Labanon bai ba mu damar jinkiri ba. Musamman yakin tunani da ke akwai a kasar Labanon.

A kowace rana, wani cikin rashin kunya sai ya zo ya haifar da yaƙin tunani a kan al'ummar Lebanon.

Sakatare Janar na kungiyar Hizbullah ta Labanon yaci gaba da cewa: Duniya ta san cewa Amurkawa za su iya tilasta Netanyahu ya daina mamaye Gaza. Gwagwarmaya ba ta da sha'awar jinkirta martani alhali yanayin shirye-shiryen makiya yana ci gaba.

Abin da muka yi a filin a matsayin gwagwarmaya ta fuskar, manufarmu, shirinmu da abin da zamu aiwatar a fagen, Mun sanya matakan da za a bi domin mayar da martini kamar haka:

1- Wanda aka nufa da hari ya kasance ba farar hula ba ne, domin mun san akwai shahidai farar hula a yankunan kudancin birnin Beirut kuma muna da yancin mu nufi wadan suke fararen hula amma mun kauda kai akai.

Tun da farko, mun yi ƙoƙarin tallafawa wajen kare farar hula a Lebanon. Ko da yake akwai shahidai farar hula, mun sami damar tallafawa wajen kare fararen hular Lebanon gwargwadon iko.

Ya ci gaba da cewa: Ina jaddada cewa babu wani makami mai linzami da sauransu da makiya suka iya lalatawa.

Wannan wani sabon rashin nasara ne a gare su. Har ila yau, da'awar sojojin makiya da ma na Netanyahu da suka lalata dubban makamai masu linzami tare da lalata dubban dandamalin harba makamai, karya ce.

Kafin azahar, ba su ce Katyusha ba, suna cewa ne ballistic, amma daga baya sun ce makamai masu linzami masu cin gajeren zango. Sai dai bayan an harba makaman roka, sun kai hari kan dandamali guda 2, amma ba su kai harin ba bayan wannan.

Muna da dubban dandamali da makamai masu linzami, duk da sun hari wasu wuraren kuma sun lalata wasu dandamali da makamai masu linzami, amma wannan ba matsala ba ne…